<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>3</hymn_number>
<title>Abu Duk A Duniya Ubanmu Ne Ya Yi LW3</title>
<lyrics>[V1]
 1) Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
 Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
 Shi ya kan ba mu ruwa a loton shukawa,
 Har amfanin gonaki ba za mu rasa ba.

[V2]
 2) Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
 Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
 Ya ba mu hasken rana, mu kama aikinmu.
 Duhun dare kyautarsa, mu riƙa hutawa.

[V3]
 3) Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
 Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci.
 Duk masu rai na duniya, ya kan ciyad da su.
 Kifaye da tsuntsaye, ya san bukatarsu.

[V4]
 4) Abu duk a duniya Ubanmu ne ya yi,
 Sai mu yi ta yabonsa, Allah Mahalicci
 Mu kuma Masu Binsa aikin hannunsa ne, Ubanmu mai ƙauna mahaliccinmu ne.</lyrics>
</song>